Uwargidan Tinubu Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Gwamnan Jihar Jigawa


Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta kai ziyara ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da mai dakinsa, Hajiya Hadiza, domin yin ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi, da ɗansa, Abdulwahab.

Tare da Uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima, da Uwargidan Kakakin Majalisar Wakilai, Hajiya Fatima Abbas, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta nuna alhini bisa wannan rashi mai girma, tare da jaddada cewa rayuwa da mutuwa duka suna hannun Allah.

A jawabinsa, Gwamna Namadi ya gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa bisa wannan ziyara ta ta’aziyya, inda ya bayyana cewa wannan ƙaddara daga Allah ce da babu makawa.

Hajiya Maryam Namadi ta rasu a ranar 25 ga Disamba, 2024, bayan fama da jinya, yayin da ɗansa, Abdulwahab, mai shekaru 24, ya rasu sakamakon hatsarin mota a ranar 26 ga Disamba, 2024.

More from this stream

Recomended