
Bayan shafe tsawon lokuta ana jiran tsammani a karshe majalisar dattawa ta sanar da sunayen da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya mika mata domin tantancewa.
Tsofaffin gwamnoni, Nasiru Elrufai, David Umahi da kuma Nyesom Wike na daga cikin jerin sunayen mutanen da Tinubu zai naɗa ministoci.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio shi ne ya karanto sunayen a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.
Ga jerin sunayen nan a kasa:
- Abubakar Momoh
- Yusuf Tuggar
- Ahmad Dangiwa
- Hannatu Musawa
- Uche Nnaji
- Betta Edu
- Doris Uzoka
- David Umahi
- Nyesom Wike
- Muhammad Badaru
- Nasir el-Rufai
- Ekerikpe Ekpo
- Nkiru Onyejiocha
- Olubunmi Ojo
- Stella Okotette
- Uju Ohaneye
- Bello Goronyo
- Dele Alake
- Lateef Fagbemi
- Mohammad Idris
- Olawale Edun
- Waheed Adebanwp
- Imaan Ibrahim
- Ali Pate
- Joseph Usev
- Abubakar Kyari
- John Enoh
- Abubakar Danladi