Tinubu Ya Godewa Buhari Da Sarkin Daura

Bola Ahmad Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagos kuma dantakarar shugaban kasa a jam’iyar APC ya godewa shugaban kasa, Muhammad Buhari saboda goyon baya da karfafa gwiwa da yake bashi.

Har ila yau Tinubu ya godewa Mai Martaba Sarkin Daura bisa addu’a da yake masa.

Tinubu ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasar ya ziyarci shugaban kasa, Muhammad Buhari a gidansa dake Daura.

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa  a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...