Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na man fetur da dangoginsa a yankin Neja Delta.
A wata sanarwa ranar Litinin, Danjuma Jonah mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar ya ce an kama mutane da dama da ake zargi da hannu a lamarin.
Jonah ya ce jiragen ruwa 54 ƙirar gida da kuma motoci da ake amfani da su wajen jigilar man aka ƙwace.
Ya ce an samu wannan gagarumar nasara ne a samame da kuma farmakin da rundunar ke cigaba da kaiwa jihohin dake yankin.