Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya roƙi ’yan Najeriya da su ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin cikar manufofinsa na samar da zaman lafiya da ci gaba a ƙasar.
Shettima ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a yayin sallar Idin Layya da aka gudanar a filin Idi na kasa da ke kan titin Filin Jirgin Sama a birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, bukin Eid al-Adha lokaci ne na tunani da sadaukarwa, wanda ke koya mana darasin biyayya da ƙwazo daga annabi Ibrahim (AS). Ya ce irin waɗannan dabi’u ne ke gina ƙasa mai ƙarfi da haɗin kai.
“Shekara ta layya lokaci ne da ya kamata mu duba halin da muke ciki, mu kai wa mabukata taimako, sannan mu gina gada tsakanin juna na ƙauna da haɗin kai,” in ji Shettima.
Ya bayyana cewa Najeriya na bukatar zaman lafiya da haɗin kai, inda ya bukaci ’yan kasa da su duba bayan bambancin da ke tsakaninsu su kuma nemi mafita ta bai daya domin ciyar da kasa gaba.
“Rayuwa kamar tseren gudu ne. A matsayinka na mutum ka iya yin sauri, amma ka gaji da wuri. Amma a matsayinmu na ƙasa, za mu iya kaiwa tudun mun tsira,” in ji shi.
Shettima ya kuma bukaci jama’a da su mara wa shugabancin Tinubu baya, yana mai jaddada cewa haɗin kai da sadaukar da kai suna da muhimmanci wajen magance matsalolin da suka haɗa da tsaro da talauci.
Shettima Ya Nemi ’Yan Najeriya Su Nuna Goyon Bayan Ga Gwamnatin Shugaba Tinubu
