NNPC Da Wasu Gidajen Mai Sun Kara Farashin Man Fetur

Kamfanin Mai na Kasa, wato Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), tare da wasu gidajen mai a Najeriya, sun kara farashin man fetur (Premium Motor Spirit).

Manema labarai da suka zagaya wasu gidajen mai na NNPCL a Abuja a ranar Talata sun gano cewa an daga farashin fetur zuwa N960 kan kowace lita, daga N875 da ake sayarwa a ranar Litinin.

Wannan na nufin kamfanin ya kara N85 kan kowace lita.

An fara aiwatar da sabon farashin a gidajen mai na NNPCL da ke kan titin Kubwa Expressway, Gwarimpa, Wuse Zone 6, Zone 4 da sauran wurare a birnin.

Haka kuma, gidajen mai na Empire da Ranoil Sharon sun kara farashinsu zuwa tsakanin N960 da N980 kan kowace lita.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gidan mai na MRS da ke kan Kubwa Expressway bai fara sayar da fetur ba.

More from this stream

Recomended

Kotun Tarayya Ta Tabbatar Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) Æ™arÆ™ashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Kotun ta yi watsi da Æ™arar da É—an majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa lamarin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa. Mai […]