NLC ta bai wa gwamnoni wa’adin kwana 19 kan mafi karancin albashi | BBC Hausa

Kafin a cimma matsayar, kungiyar kwadagon ta bukaci a yi wa ma'aikatan da ke karbar albashin da ya haura naira 30,000 karin kashi 29 cikin 100

Hakkin mallakar hoto
@FKEYAMO

Image caption

A baya kungiyar kwadagon ta zargi gwamnati da jan kafa wurin biyan sabon mafi karancin albashin

Hadaddiyar kungiyar kwadago a Najeriya ta gargadi gwamnonin kasar da su fara biyan sabon mafi karancin albashi na naira 30,000 kafin 31 ga watan Disamban nan da muke ciki.

Kungiyar ta yi wannan gargadi ne a wata sanarwar bayan taro da ta fitar na masu ruwa da tsakin kan sabon albashin.

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya bukaci jihohin da ba su fara biyan sabon albashin ba su gaggauta kammala tattaunawa da sauye-sauyen da ake bukata kafin cikar wa’adin na 31 ga watan Disamban da muke ciki.

Kunigyar kwadago ta NLC ta yi gargadin cewa rashin yin hakan kafin cikar wa’adin na iya haifar da mummunan sakamako da ba za ta iya bayar da tabbacin kawarwa da shi ba.

Mahalarta taron sun yanke shawarar yin aiki tare wajen tabbatar da aiwatar da biyan sabon mafi karancin albashin yadda ya kamata.

Sun tattauna kan sauye-sauyen da za a yi kan albashin ma’aikata bayan amincewar gwamnatin tarayya da naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar.

Taron ya samu halarcin shugabannin kungiyar na jihohi da takwarorinsu na kuniygar ma’aikata ta TUC da ministan ayyuka da wakilan gwamnatin tarayya da hukumar kwadago ta duniya.

Jihohin Adamawa da Jigawa da Kaduna da Kebbi da Legas sun kammala aiki a kan fara biyan sabon albashin, amma har yanzu Jigawa ba ta fara biya ba tukuna.

Wasu jihohi kuma sun kafa kwamitin tattaunawa da kungiyar kwadagon kan sauye-sauyen da suka shafi biyan sabon albashin.

Jihohin su ne Abia da Akwa Ibom da Bayelsa da Borno da Ebonyi da Edo da Kano da Katsina da Neja da Ondo da Sokoto da Kuma Zamfara.

Wadanda ba su riga sun kafa irin wannan kwamiti ba su ne jihohin Bauchi da Yobe da Rivers da Benue da Gombe da Kwara da Imo da Osun da Ekiti da Oyo da Anambra da Taraba da Cross River da Ogun da Enugu da Nasarawa da Plateau da Kogi da kuma jihar Delta.

More News

Hoto:Kwankwaso Ya kaddamar da wasu ayyuka a Kaduna

Biyo bayan gayyatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi masa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu...

Sarkin Kano Aminu Ado ya zama uba ga Jami’ar Calabar

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu girmamawa bayan an nada shi a matsayin uban Jami'ar Calabar da ke Jihar Cross...

Za a yi Ruwan Sama a Wasu Garuruwan Adamawa —Mai hasashe

Wani mai hasashen yanayi a Najeriya Alhaji Adamu Katakore ya faɗa cewa za yau Alhamis za a samu ruwan sama a wasu garuruwan jihar...