Najeriya: Rundunonin tsaron da ba sa ƙarƙashin gwamnatin Tarayya

Amotekun

Asalin hoton, @Amotekun Facebook

Bayan Amotekun a yankin ƙabilar Yarabawa yanzu kuma an samar da rundunar Ebube Agu a yankin ƙabilar Igbo a kudancin Najeriya.

Tun ɓullar Boko Haram a yankin arewaci, aka fara samar da ƴan sa-kai da ake kira Civilian JTF a jihar Borno da ke taimaka wa jami’an tsaro yakar ƴan Boko Haram.

Kafa rundunonin ya ƙara fito da girman ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, dalilin da ya sa yankunan kudancin ƙasar suka samo wa kansu mafita.

Kawo yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ce komai ba game da kafa rundunar tsaro ta Ebube Agu a yankin Igbo bayan kafa Amotekun ya janyo ce-ce-ku-ce inda har gwamnatin tarayya ta haramta rundunar.

‘Ebube Agu’

Asalin hoton, HOPE UZODINMA/FACEBOOK

Bayanan hoto,
Taron gwamnonin kudu maso gabas a Najeriya

A ƙarshen makon da ya gabata ne gwamnonin jihohin kudu masu gabas suka yanke shawarar kafa runduna ta musamman domin tunkarar matsalar tsaro a yankinsu.

Gwamnonin da suka ƙunshi na Anambra da Abia da Ebonyi da Enugu da kuma Imo sun raɗawa sabuwar rundunar sunan “Ebube Agu” da ke nufin “A ji tsoron zaki.”

Sun ce an dora wa rundunar da hedikwatarta za ta kasance a Enugu, alhakin kula da ayyukan ƴan banga da yankin kudu maso gabas da kuma magance duk wani yunƙurin tashin hankali a yankin.

Matakin kafa rundunar na zuwa ne bayan hare-hare da dama da aka kai wa jami’an tsaro da ƙone ofisoshin ƴan sanda cikin kwana hudu a jihar Imo da kuma sace-sacen mutane a yankin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Har da mata aka ɗauka a rundunar Amotekun

Amotekun rundunar tsaro ce a yankin kudu maso yammacin Najeriya ce da aka kafa a watan Janairun 2020 a wani taron da shugabannin yankin suka gudanar a Ibadan da ke jihar Oyo.

Aikin rundunar ya shafi kula da tsaron jihohi shida na shiyyar kudu maso yammacin Najeriya. Kuma Amotekun ita ce runduna ta farko da wani yanki a Najeriya ya kafa domin kula da sha’anin tsaro.

Amotekun da kalmar Yoruba na nufin damisa, kuma aikin rundunar ya shafi kula da tsaron dukkanin jihohin kudu maso yammacin Najeriya da suka haɗa da Oyo da Legas da Ogun da Ondo da Osun da kuma Ekiti.

Kuma aikin Amotekun ya shafi taimaka wa ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya wajen yaƙi da ta’addanci da fashi da makami da satar mutane domin kuɗin fansa da kuma tunkarar rikicin makiyaya da manoma a yankin.

Dukkanin jihohin na shiyyar kudu maso yammaci ne za su ɗauki nauyin kula da rundunar samar da kayan aiki.

Tuni aka ƙaddamar da rundunar a jihohin Legas da Ekiti da Osun tare da ba su bindiga harba ruga irin ta mafarauta.

‘Ƙato da Gora’

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Ƴan Kato da Gora ke kula da wasu shingayen bincike a Borno

Ƙato da Gora ko ƴan sa-kai wato CJTF an kafa su ne yankin arewa maso gabashin Najeriya domin yaƙar Boko Haram a jihohin Borno da Yobe.

Ƴan JTF suna taimakawa sojoji yaƙi da Boko Haram inda aka ba su makamai tare da biyan su albashi.

A baya gwamnatin Nigeria ta ce za ta soma ɗaukar ƴan ƙato da gora masu taimaka wa sojan kasar wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ka fi sani da civilian JTF, aikin soja.

Rikicin Boko Haram ya hallaka dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...