Wani matashi mai suna Auwalu Salisu dan shekara 22, ya mayar da naira miliyan 15 da wani fasinja ya manta da shi.
Fasinjan dai ya zo ne daga kasar Chadi don sayen kaya a Kano sai kuma ya manta da shi.
Salisu wani mazaunin Yankaba da ke karamar hukumar Nasarawa a cikin babban birnin jihar, ya mayar da kudin ne bayan ya ji sakon bacewar kudin a wani gidan rediyo da ke Kano.
Kudaden wadanda sun kai maira miliyan 15 idan aka canza su, sun hada da; CFA miliyan 10.130 da kuma Naira miliyan 2.9.
Da yake zantawa da gidan rediyon Arewa a Kano, ya ce bai lura fasinjan nasa ya manta da kudin ba har ya isa gida.
Ya ce bayan gano kudin ne ya sanar da iyayensa wadanda suka umarce shi da ya je ya nemo mai shi.