Majalisar wakilai za ta samar da jami’ar Bola Ahmad Tinubu

Ƙudurin kafa dokar kafa Jami’ar Karatun Yaruka Ta Bola Ahmad Tinubu ya tsallake karatun farko a majalisar wakilai ta tarayya.

Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu da kuma wasu ƴan majalisar su 8 da suka haɗa da  Inuwa Garba, Nasiru Shehu, Alex Ikwechegh, Bako Useni, Amobi Ogah, Akin Rotimi, Halims Abdullahi, da Felix Nwaeke su ne su ka gabatar da kuɗirin dokar.

Jami’ar da za a kafa a garin Aba dake jihar Abia  za ta yi ƙoƙarin bunƙasa karatu da kuma amfani da yarukan Najeriya da kuma al’ada domin cigaban ƙasa.

Jami’ar za ta mayar da hankali wajen samar da yana yi mai kyau domin karantar kwasakwasan digiri da kuma difloma.

Ƙudurin dokar na buƙatar tsallake karatu na biyu da na uku kafin majalisar dattawa itama ta amince da shi kana a miƙawa shugaban ƙasa.

Related Articles