Likitoci a Abuja sun tafi yajin aiki na kwanaki uku

Ƙungiyar Likitoci Ma’aikatan Gwamnati ta Birnin Tarayya (ARD FCTA) ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku saboda rashin biyan albashi, alawus, da wasu buƙatu da ba a cika ba.

Wannan yajin aikin ya tsayar da duka ayyukan asibitocin gwamnati a Abuja.

Shugaban ARD FCTA, Dakta George Ebong, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana ranar Laraba a Abuja.

Dakta Ebong ya ce yajin aikin ya biyo bayan wa’adin makonni uku da suka bayar tun bara, wanda ya ƙare ba tare da ɗaukar mataki ba.

A cewarsa, likitoci a Abuja sun zama tamkar “ma’aikata da aka watsar,” inda ya roƙi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya shiga tsakani don hana yajin aiki na dindindin.

Ya ƙara da cewa shawarar yin yajin aikin gargadi ta kwanaki uku ta samo asali ne daga taron ƙungiyar da aka yi ranar Talata.

“Wannan yajin aikin yana gudana a duk asibitocin gwamnati da ke Abuja—daga Wuse, Asokoro, Maitama, Kubwa, Zuba, Kwali, Abaji, Nyanya, da sauran su.

“Mun bai wa gwamnati wa’adin makonni uku don ta biya bukatunmu, amma bayan haka mun yi tarurruka da dama. Sun roƙi makonni biyu na ƙarin lokaci, amma har yanzu babu wani abu da aka yi. Ba ma mafi ƙanƙantar mataki ba. Mun yi tsammanin za su biya bashin watanni shida na albashi da ake binsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan har ba a ɗauki matakin gaggawa ba bayan kwanaki uku, za su koma yajin aikin dindindin.

A watan Disamba da ya gabata, ƙungiyar ARD FCTA ta yi gargadin yajin aiki saboda rashin biyan buƙatunta.

More from this stream

Recomended