Labarin wasanni: Madrid za ta musanya Bale da Pogba, Palace ba ta son sakin Zaha

Gareth Bale da Pogba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An dade ana hasashe kan makomar Bale da Pogba a Real Madrid da Manchester United

Real Madrid a shirye take ta bayar da Gareth Bale mai shekara 29 domin karbo Paul Pogba daga Manchester United mai shekara 26, in ji jaridar Mail.

Sai Manchester United ta biya fam miliyan 90 idan har tana son sayen Harry Maguire mai shekara 26 daga Leicester City – inda dan wasan na Ingila zai kasance dan wasan baya mafi tsada a tarihi, a cewar Telegraph.

Manchester United ta nuna sha’awar dan wasan Spain Dani Olmo da ke taka leda a Dinamo Zagreb mai shekara 21, in ji Daily Mail.

Crystal Palace ba ta son sayar wa Arsenal dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 26, in ji Daily Mirror.

Akwai yiyuwar Alexandre Lacazette, mai shekara 28 zai bar Arsenal kafin rufe kasuwar musayar ‘yan wasa, a cewar Express.

Atletico Madrid na son dauko Lacazette domin maye gurbin Antoine Griezmann, mai shekara 28 idan ya koma Barcelona, in ji Daily Mirror.

Barcelona na jiran tayin dan wasanta na baya Samuel Umtiti, mai shekara 25, wanda Manchester United ke son saya, in ji Sport, via Mirror.

Dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 22, yana son ci gaba da taka leda a Barcelona duk da manyan kungiyoyi sun nuna suna sha’awarsa kamar Liverpool da Bayern Munich, a cewar jaridar L’Equipe.

Aston Villa tana son sayo dan wasan Kasimpasa dan kasar Masar Mahmoud Trezeguet, mai shekara 24, in ji jaridar Sun.

More News

Gobara ta kama wani sashe na kotun ƙolin Najeriya

An samu tashin gobara a wani sashe na Kotun Kolin Najeriya dake birnin tarayya Abuja. Kawo yanzu babu wani bayani kan musabbabin tashin gobarar amma...

Gobara ta kama wani sashe na kotun ƙolin Najeriya

An samu tashin gobara a wani sashe na Kotun Kolin Najeriya dake birnin tarayya Abuja. Kawo yanzu babu wani bayani kan musabbabin tashin gobarar amma...

Yan bindiga sun sace kwamishinan yaɗa labarai na Benue

Yan bindiga sun yi garkuwa da, Matthew Abo Kwamishinan Yada Labarai, Al'adu da Yawon Bude Ido na jihar Benue. An yi garkuwa da Abo a...

Nan bada jimawa za a kawo karshen rashin wutar lantarki a Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta roki mazauna jihar da su kara hakuri inda ta ce rashin wutar lantarki da ake fuskanta a jihar zai zo...