
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN tayi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da kuma ta tarayya da su binciki dalilin rugujewar wani bangare na babban masallacin Juma’a na Zaria.
Shugaban kungiyar CAN, Daniel Okoh shi ne yayi wannan kira a cikin wani sakon ta’aziyya ga al’ummar Musulmin Zaria.
A cikin sanarwar da aka fitar a Abuja Okoh ya ce binciken zai taimaka wajen kare faruwar irin haka anan gaba kana yayi kira ga gwamnati ta tabbatar da ta samar da kariya a wuraren ibada.
Okoh ya bayyana tausayinsa da jimaminsa ga al’ummar musulmi dama gwamnatin jihar inda yayi addu’ar juriya ga iyalan wadanda suka mutu.
Mutane da dama ne dai suka mutu bayan da wani sashe na ginin masallacin ya ruguzo lokacin da ake tsaka da sallar Juma’a.