Kashim Shettima: Buhari ba shi da isassun kayan yaƙi da ƙungiyar Boko Haram

Tsohon gwamnan Borno Sanata Kashim Shettima
Bayanan hoto,
Tsohon gwamnan ya ce rashin hadin kai da nuna kishin kai na daga cikin matsalolin da suka addabi arewacin Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Kashim Shettima ya ce babu isassun kayan da sojojin kasar ke bukata domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Sanata Shettima, wanda yanzu dan majalisar dattawa ne, ya yi gwamnan jihar Borno na shekaru 8, lokacin da ake tsaka da rikicin Boko Haram.

Ya yi kalaman ne a taron da kungiyar musulman Najeriya ta gudanar ranar Lahadi.

Kashim Shettima ya ce: “Kayan yakin da ake magana za a iya samunsu a Afirka ta Kudu ko Turkiyya ko Indiya ko Ukraine – za a same su a kasashe babu iyaka, kuma sojoji sun a da kuzari amma babu kayan aiki.

Boko Haram suna shan tramadol su kai wa sansanin sojoji hari. Abin da nake son fada shi ne muna bukatar a dauki matakan da suka dace, mataki na sojoji, da na tattalin arziki, da daukar mataki na kashin kamu,” in ji tsohon gwamnan.

A cewarsa, shugaban Najeriya ya gaza cimma wasu daga cikin muradunsa ne saboda ba ya bincike kan abubuwan da mutanen da ya nada a kan mukamai suke yi.

“Fisabilillahi nake fada, kawaicin shugaba kasa ya wuce gona da iri, sai ya nada mutum a mukami amma ba tare da tuntuba ba sai a bar mutum kara zube.

Shi mutumin da ne yana ganin kamar kowa kamar shi ne sannan kowa zai yi aiki. Ya kamata ya tabbatar da cewa duk kudin da aka ware domin sayen kayan aiki an saya amma wallahi tallahi maganar gaskiya babu kayan aiki,” a cewar Shettima.

Ya kara da cewa ya hadu sa sabon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Janaral Attahiru, ya kuma nuna kuzari wajen aiki “kuma muna fatan nan ba da jimawa ba za a samu maslaha kan halin da ake ciki.”

Shettima ya ce ana bukatar sanin ta yadda za a farfado da tattalin arzikin arewacin Najeriya, saboda baki daya motocin tarakta 44,000 kadai ake da su a kasar, yana mai cewa “amma a jihar Uttar Pradesh da ke kasar Indiya suna da tarakta miliyan biyu da dubu dari uku.”

A cewarsa “duk irin hakilon da ake yi na inganta noma babu kayan aiki; akwai wani gwamna a arewacin Najeriya muna hira da shi na tambaye shi tarakta nawa yake da su ya ce ba su kai guda 20, kuma wai ita ce jihar da ake cewa ta na sahun gaba wajen samar da abinci.

Akwai wanda na tambaya injin cashe shinkafa nawa ake da su a jihar Kebbi? Aka ce min guda daya ne na gonar Sanata Adamu Aleiro, ban da shi babu wani inji a jihar. Dole ne mu rungumi fasahar zamani, kuma ba mai tsada ba ne, sannan muna da kwararrun yara da za su ilmantar da mutanenmu, saboda arewa ba mu da kasuwanci talauci ya mana katutu.”

Tsohon gwamnan na jihar Borno ya kara da cewa babban abin da ake bukata shi ne hadin kai domin kawo zaman lafiya.

“Rashin gaskiya, da rashin hadin kai da son zuciya, da duba abin da mutum zai samu na kashin kansa a kan me mutanenmu za su samu na zaman lafiya, shi ne babban matsalarmu. Muddin muka sanya cewa zaman lafiya shi ne a sahun gaba na abin da muke butaka to Insha Allah za a samu zaman lafiya. Sai kuma batun ilimi, samar da ilimi yana da matukar muhimmanci da inganta shi,” in ji Shettima.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...