Kalubale 10 da ke gaban Lionel Messi |BBC

Lionel Messi

Hakkin mallakar hoto
FCBarcelona

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Argentina da Barcelona, Lionel Messi ya yi bajinta da yawa a fagen taka leda a duniya da za a dade ana tunawa da shi.

Ciki har da lashe Ballon d’Or shida da karbar takalmin zinare a yawan cin kwallaye a Turai da sauransu, sai dai duk da haka akwai kalubale dake gabansa guda 10.

1. Tarihin yawan buga wa Barcelona wasanni.

Ba a dade ba Messi ya haura tarihin da Andres Iniesta ya kafa, ya koma na biyu a jeren wadanda suka yi wa Barca wasanni da dama, yanzu ya yi 692, wanda ke na daya shi ne Xavi Hernandez wanda ya buga 767.

2. Takalmin zinare na bakwai a La Liga da Turai

Messi ya lashe takalmin zinare karo na shida wajen cin kwallaye a gasar Turai, kuma a lokacin kan jagoranci zura kwallaye a raga a gasar La Liga.

3. Yawan lashe kofuna da Ryan Giggs da Vitor Baia suka yi

Idan har Barcelona za ta ci kofuna uku nan gaba, hakan zai bai wa Messi damar haura tsohon dan wasan Manchester United Ryan Giggs mai horas da tawagar Wales a tarihin da ya kafa.

Kawo yanzu ya dara tsohon golan Barcelona da kungiyar Porto Vitor Baia da kofi daya.

4. Lashe kofin Champions League biyar

Za a buga wasan karshe na Champions League a bana a filin wasa na Ataturk da ke Istanbul, idan har Barcelona ta lashe kofin shi ne karon farko da Messi zai daga a matsayin kyaftin, kuma na biyar jumulla.

5. Dan Barcelona da ya fi yawan buga El Clasico

Xavi Hernandez ne ke rike da tarhin yawan buga wa Barca wasan hamayya na El Clasico, sai dai Messi wanda ya yi karawa 41, idan ya buga wanda za a yi ranar 26 ga watan Oktoba zai yi kan-kan-kan da na Hernandez.

‘Yan wasan Real Madrid uku sun buga El Clasico 42 daidai da na Xavi, inda Sergio Ramos har yanzu ke buga wasannin daga cikin sauran.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

6. Cin kwallo daga bugun tazara sau 50

Lionel Messi ya kusan cin kwallo na 50 a bugun tazara, kawo yanzu yana da 43 a Barcelona da guda shida da ya ci wa Argentina.

7. Cin kwallo uku rigis a bugun tazara

Messi ya ci kwallo biyu a bugun tazara a karo da dama, idan har zai samu damar cin uku a wasa guda, hakan zai kara daga darajarsa a tamaula.

8. Cin kwallo 500 a gasar Lik

Kyaftin din Argentina ya haura 400 da ya zura a raga a bara, kawo yanzu ya ci 420 a La Liga.

Wanda ke kan gaba shi ne Josef Bican da yake da 447, sai kuma Uwe Seeler mai guda 444 a raga.

9. Doke yawan kwallon da Pele ya ci a tarihi

An ce Pele ya zura kwallo 510 zuwa 643 har da 31 da ya ci a Cosmos ta New York, Messi yana da 604 da ya ci a Barcelona kawo yanzu.

10 Cin kwallo 700

Messi ya ci kwallo 672 jumulla, guda 604 a Barcelona da 68 a tawagar Argentina, daf ya ke da ya kai 700 kenan idan yana da koshin lafiya.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...