Jami’an tsaro sun halaka ƴan bindiga a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun gudanar da wani samame da suka yi nasara a dajin Yankari, inda suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga 10 tare da ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su.

Wannan farmakin mai suna Operation Sharar Daji, ya nuna gagarumar nasara wajen yaki da miyagun laifuka a yankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

A cewar Wakili, wannan farmakin ya samo asali ne sakamakon kiraye-kirayen da al’ummar garin Gaji suka yi, wadanda suka afka cikin mummunan harin da masu garkuwa da mutane 24 suka kai ranar Alhamis.

Wadanda abin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne da suka dawo daga Kasuwar Mararaban Liman Katagum.

Maharan sun dauke su da karfi tare da kai su wani wuri da ba a bayyana ba a cikin dajin Yankari, wanda aka fi sani da Red Mountain.

More News

Mutane 8 sun mutu a hatsarin mota akan hanyar Abuja-Lokoja

Fasinjoji 8 aka tabbatar sun mutu wasu biyu kuma suka jikkata bayan da wata motar fasinja ƙirar  ta daki wata babbar mota a kusa...

Mutane 9 sun mutu wasu 3 sun jikkata a hatsarin mota a Kano

Mutanen da basu gaza 9 ne ba suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Kano zuwa Zaria a...

Ƴan bindiga sun nemi kudin fansa N30m da babura kan ɗan takarar kansila da suka sace a Kaduna

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani dan takarar kansila mai suna Japheth Zarma Yakubu a unguwar Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia...

Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari a Maiduguri

Ana fargabar tserewar fursunoni biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye gidan yari a birnin Maiduguri. Aƙalla fursunoni 200 ake kyautata zaton sun tsere daga...