Jami’an tsaro sun halaka ƴan bindiga a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun gudanar da wani samame da suka yi nasara a dajin Yankari, inda suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga 10 tare da ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su.

Wannan farmakin mai suna Operation Sharar Daji, ya nuna gagarumar nasara wajen yaki da miyagun laifuka a yankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

A cewar Wakili, wannan farmakin ya samo asali ne sakamakon kiraye-kirayen da al’ummar garin Gaji suka yi, wadanda suka afka cikin mummunan harin da masu garkuwa da mutane 24 suka kai ranar Alhamis.

Wadanda abin ya rutsa da su ‘yan kasuwa ne da suka dawo daga Kasuwar Mararaban Liman Katagum.

Maharan sun dauke su da karfi tare da kai su wani wuri da ba a bayyana ba a cikin dajin Yankari, wanda aka fi sani da Red Mountain.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...