Hukumar NDLEA Ta Lalata Magungunan Da Suka Yi Isfaya a Jigawa

Hukumar Yaki da Shan Magungunan Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), a hadin gwiwa da Kungiyar Magungunan Kimiyya, ta lalata magungunan da suka dade a ajiye a jihar Jigawa, wanda darajarsu ta kai sama da N800,000 a yankin Karamar Hukumar Gumel.

Shugaban Karamar Hukumar Gumel, Alhaji Lawan Ya’u Abdullahi, ya bayyana wannan lokacin taron a Gumel. Ya jaddada kudurin hukumar na kare lafiyar jama’a, yana mai da hankali kan muhimmancin hadin kai wajen gina al’umma mai lafiya.

A cewar Malam Bashari Dahiru Gagarawa, shugaban reshen kungiyar magungunan kimiya na yankin, ya gode wa gwamnatocin jiha da karamar hukuma bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen inganta harkokin lafiya.

More from this stream

Recomended