Shirin Auren Zaurawa (wato ‘Mass Wedding Initiative’ a Turance) zai laƙume Naira Miliyan 854 daga aljihun Gwamnatin Jihar Kano.
A cewar gwamnatin, an amince da hakan ne a ranar Laraba a taron majalisar zartarwa na jihar, duba da yanayin tattalin arzikin kasar.
Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar ne ya sanar da hakan a shafin sa na X, wanda aka fi sani da Twitter, ranar Alhamis.
Ya rubuta, “Kuma daga taron jiya, majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da fitar da zunzurutun kudi har naira miliyan 854 na kashi na farko na shirin bikin aurar da zaurawa.
“Da kuma Naira Miliyan 700 na kudin karatu na dalibai 7000 na Jami’ar Bayero Kano (BUK).”
Idan dai za a iya tunawa, gwamnan ya kuma ware wa dalibai ‘yan asalin jihar Kano 7,000 a Jami’ar Bayero Kano (BUK), wadanda za su karbi Naira miliyan 700 domin biyan kudin karatunsu.