Gobarar Tankar Mai Ta Yi Ajalin Mutane Da Dama A Enugu

A kalla mutanen 11 ne suka rasa rayukansu lokacin da wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a kan titin Enugu-Onitsha a ranar Asabar.

Tankar, wanda ta samu matsalar taya, ta fadi, sannan ta zubar da abinda ke cikinta kafin ta fashe.

Gwamna Peter Mbah, wanda ya yi magana game da wannan mummunan lamari, ya ce wadanda suka ji rauni suna samun kulawar likita, sannan jihar za ta dauki matakan da suka dace domin kaucewa sake faruwar irin wannan hadari a nan gaba, ciki har da tabbatar da bin dokokin tituna da gyara sassan titin tarayya da ke cikin tsaku.


Mbah ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka ji rauni.

More from this stream

Recomended