Egypt ta yi waje da Kamaru a gasar AFCON

‘Yan wasan Egypt sun samu nasarar cire I kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka a gasar ta AFCON.

Hakan na nufin kasar ta Masar ta kai wasan karshe.

Egypt ta yi nasara ne da bugun fenariti da ci 3-1 bayan da aka kwashe minti 120 babu wanda ya zura kwallo.

Yanzu ‘yan wasan na Masar za su hadu da Senegal wacce tuni ta kai zagayen wasan karshe.

‘Yan wasan Kamaru sun zubar da fenariti uku a bugun daga kai sai mai tsaron gidan yayin da Egypt kuma ta ci duka wadanda ta buga.

Yanzu Kamaru za ta hadu da Burkina Faso don neman matsayi na uku a gasar ta AFCON wacce ake yi a karo 33.

Bangarorin biyu sun yi ta fafatawa cikin zagayen farko da kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, amma babu wanda ya kai ga gaci ta hanyar cin kwallo.

More News

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...

‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...