Boeing ya dakatar da kera jirgin 737 Max | BBC news

@

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kamfanin jiragen sama na Boeing zai dakatar da kera samfurin jiragensa na 737 Max a farkon shekarar 2020 mai kamawa.

A baya Beoing ya cigaba da kera jiragen 737 Max, bayan dakatar da tashin jiragen na tsawo wata tara, sakamakon wasu munanan hadura da jiragen suka yi.

Akalla mutum 300 ne suka mutu a hadarin da wasu jiragen Beoing 737 Max suka yi a Indonesia da Ethiopia sakamon wata sabuwar matsala.

Kamfanin ya yi fatan ci gaba da kera samfurin jiragen a karshen shekarar nan ta 2019.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka ta sheda wa Boeing cewa ba za a yi sauri wurin ba wa jiragen izinin fara tashi ba.

Boeing wanda ke daga cikin kamfanonin Amurka da ke fitar da kaya zuwa kasuwannin duniya, ya ce ba zai sallami ma’aikatansa da ke da alaka da jiragen 737 Max. Sai dai da alama dakatar da jiragen na iya yin tasiri a kan dillalai da ma tattalin arzikin kasar.

Me ya samu jiragen 737 Max?

A makon jiya ne aka sheda wa majalisar dokokin Amurka cewa bayan hadarin 737 Max a Indonesia a 2018, hukumomin kula da sufurin jiragen saman Amurka na da masaniyar cewa akwai barazanar samuwar karin hadarin jiragen a nan gaba.

Kwararrun hukumar sun yi hasashen yiwuwar samun gomman haduran jiragen, matukar ba’a yi wa taswirar jiragen gyare-gyare ba.

Amma duk da haka ba’a dakatar da 737 Max daga tashi ba, sai bayan hadarin jirgin na biyu a Ethiopia a watan Maris na 2019.

Boeing na sauya taswirar na’urar da ke sarrafa kanta a jirgin, wadda ake gani ita ce ke haifar da matsalar.

Kamfanin ya ce yana da jiragen 737 Max guda 400 a rumbun ajiyarsa, kuma zai mayar da hankali wajen mika jiragen ga wadanda suka saye su.

Yayin da wasu kamfanoni sun riga sun yi odar jiragen, Boeing ta dakatar da mika masu jiragen har sai injiniyoyinta sun kammala gyara a kan manhajar jiragen.

Yaya ake gani?

Mai sharhi a kan masana’atu Henry Harteveldt ya ce ba’a taba ganin irin matakin na dakatar da kera 737 Max ba. Yana kuma iya yin “tasiri sosai a kan Boeing mai kera jiragen, da masu dillanci da kuma kamfanonin sufurin jiragen sama”.

“Tabbas za ta haifar da rudani ga kamfonin jirgin sama da ke da hannu a ciki da kuma kimanin kamfani 600 da ke harkar sayar da 737 Max da kamfanin Boeing kansa”.

Tuni dakatar da 737 Max ya riga ya sa Boeing asarar kusan dala biliyan tara. Ranar Litinin, hannun jarin Boeing ya karye da kashi hudu cikin dari, bayan hasashen dakatar da kera jiragen.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An dakatar da jiragen Boeing 737 Max daga tashi

Ana sa ran dakararwar za ta yi tasiri a kasuwar jirage ta duniya.

Mai sharhi kan harkokin jiragen sama na Teal Group Richard Aboulafia, ya kwatanta matakin da Boeing ya dauka a matsayin mara dadi.

Ya ce da Boeing ya mika musu jiragensu, ko kuma ya mayar masu da kudadensu har sai an yarje wa jiragen su rika tashi.

Kamfanonin jiragen sama na Amurka sun fi amfani da 737 Max, duk da cewa ana amfani da jiragen a sassan duniya.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...