AU ta koka da karancin rigakafin corona

Wakilin Kungiyar tarayyar Afirka ya ce nahiyar na cikin tsaka mai wuya na rashin allurar riga-kafin cutar corona a daidai lokacin da kasashen yankin ke fuskantar barazanar bullar kashi na uku na wani sabon na’uin annobar.

Wakilin Mista Strive Masiyiwa, ya zargi Turai da jan kafa wajen cika alkawuran yin raba daidai na rigakafin a karkashin shirin nan na COVAX na tallafawa kasashe marasa karfi da rigakafin cutar.

Ya ce, an tsara cewa Afirka za ta karbi allurar kimanin miliyan 700 kafin watan Disamban wannan shekara da muke ciki, amma kawo yanzu, allurar miliyan sittin da biyar aka samu, wannan na nufin kashi daya kacal cikin dari na al’ummar nahiyar kadai aka yi ma rigakafin cutar.

Nahiyar mai al’umma sama da biliyan daya na fuskantar barazanar yaduwar sabon na’uin na corona da aka ce na tattare da hadarin gaske ga dan adam. Matsalar da aka fuskanta, ba ta rasa nasaba da kin cika alkawura na tallafin kudin coronar da wasu daga cikin kasashen Turan suka dauka.

More News

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...

‘Kyale kowa ya mallaki makami a Zamfara na da haɗari’

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...

Hotunan Daurin Auren Dan Gwamnan Nasarawa

Manyan baki da dama ne ciki har da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suka halarci daurin auren dangidan gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da...