An sauya wa Masallacin Sheikh Mohammad Bin Zayed da ke gundumar Al Mushrif ta birnin Abu Dhabi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, suna zuwa ‘Mariam, Umm Eisa,’ da ake fassarawa ‘Maryamu Uwar Yesu’.
Canjin wanda yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Mohammad Bin Zayed Al Nahyan ya jagoranta, na da niyyar karfafa alaka tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Babban limamin cocin Andrew Thompson daga Cocin St Andrew’s ya nuna sha’awar bikin da aka yi na mahimmancin Maryamu, yayin da ta nuna alamar sadaukarwa ga Allah.
Har ila yau, Jeramie Rinne, babban limamin cocin Evangelical Community Church da ke Abu Dhabi, ya yaba da sauya sunan masallacin a matsayin nunin juriya na addini, wanda ya yi daidai da kudurin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na yin zaman tare cikin lumana.