An rantsar da Monday Okpebholo a matsayin gwamnan jihar Edo

An rantsar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin sabon gwamnan jihar Edo.

Sanata Okpebholo na jam’iyar PDP ya kayar da manyan abokanan takararsa da suka haɗa da Barista Asue Ighodalo na jam’iyar PDP da kuma Olumide Akpata na jam’iyar LP a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 21 ga watan Satumba.

Har ila yau an rantsar da Hon Denise Idahosa a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Alƙalin alƙalai na jihar, Daniel Okongbowa shi ne ya lakana masu rantsuwar kama aikin, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima shi ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya ya zuwa wajen bikin rantsuwar.

Shettima ya samu rakiyar wasu gwamnonin jam’iyar APC da suka haɗa da Ahmad Aliyu na jihar Sokoto, Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos, Dapo Abiodun na jihar Ogun da kuma Hope Uzodinma na jihar Imo.

More from this stream

Recomended