An kawon karshen cutar Kwalara a Maradi

Bachir Salifou Maï Sanda, Jami'in WASH na l'ONG CISP

Hakkin mallakar hoto
UNICEF

Image caption

Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da sauran kungiyoyin agaji sun yi nasara wajen yaki da cutar kwalara a jihar Maradi da ke jamhuriyar Nijar.

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen Afirka da cutar kwalara ke saurin kisa.

A shekarun 2010 da 2018 an samu barkewa annobar wannan cutar a mafi yawan jihohin kasar irinsu Tillabery da Maradi da Dosso da Tahoua da kuma Zinder.

Ana samun barkewar annobar daga wannan shekara zuwa waccen, daga wannan jiha zuwa waccan.

A shekarar 2010 an samu mutum 15,563 da suka harbu da cutar, kuma 426 daga cikinsu sun rasa rayukansu.

Hakazalika a shekarar 2018, mutum 3,822 ne suka harbu da wannan cuta, inda 78 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Kodayake a wannan shekarar ta 2018, Maradi kadai ta kwashe kaso 90 cikin 100 na mutanen da suka kamu yayin da cutar ta yi ajalin mutum 42.

Asibitin garin Madarounfa na jihar ta Maradi ne wannan matsala tafi shafa, inda nan kadai aka samu mutum 2640 da suka harbu da wannan cuta kuma cikinsu 42 suka bakunci lahiya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hakan ya sa UNICEF mayar da hankali kan wannan cuta a jihohin kasar hudu, inda ta samar da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen yaki da cutar.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...