An kashe Usman Buda, wani mahauci ne a Abattoir na Sokoto, sakamakon zarge-zargen da ake masa na zagin Manzon Allah (SAW).
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kisan bayan da aka yi mata waya da misalin karfe 09:20 na safe.
Da aka samu kiran, kwamishinan ‘yan sandan tare da wasu jami’ai, nan take suka amsa suka isa wurin.
Nan take aka kai shi asibitin koyarwa na Usmanu Danfodio Sokoto (UDUTH) domin yi masa magani amma ya mutu sakamakon raunin da ya samu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta fara gudanar da bincike domin cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani makwabcin marigayin wanda ya bayyana sunansa da Malam Yusuf a cikin jimami.
Ya ce mutuwar mahaucin abin damuwa ne. Ya ce, “Usman makwabcina ne. Shi mai addini ne, hasali ma dan Izala ne. Mun yi Sallah tare da halartar Tafsiri a Primary board quarters. Babu yadda za a yi ya yi irin wannan magana ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
“Dole ne a sami dalilin kashe shi. Domin ya shahara a sana’arsa ta sayar da kayan ciki na saniya kuma abokan aikinsa da dama sun yi masa hassada.”