An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin shi ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.

Ya ce mutanen da aka kama sune Sunday Nwabufor mai shekaru 47 mazaunin unguwar FESTAC da kuma Obinna Nweke mai shekaru 45 mazaunin unguwar Ketu dake yankin Mile 12.

Jami’an ƴan sandan daga ofishin ƴan sanda na Ojo ne suka kama mutanen a ranar 18 ga watan Satumba biyo bayan wasu bayanai da suka samu akan mutanen.

Ƙulli 120 aka same su da shi a yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.

More from this stream

Recomended