An kama shugaban firamare da laifin sayar da ƙarafen kujeru a Kano

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama shugaban makarantar firamaren Gaidar  Makada dake ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar kan zarginsa da ake na sayar da kayan makarantar.

A wata sanarwa mai ɗauke da sahannun, Kabir Abba Kabir mai magana da yawun hukumar da aka fitar ranar Asabar ta ce an kama shi ne bayan da aka bankaɗo wani tsari mai ban tsoro na yadda ake sayar da muhimman kayayyakin makarantar.

Ya ce hukumar na binciken lamarin kana ana cigaba da ƙoƙarin gano kadarorin da aka sayar.

” Bincike ya gano cewa kayayyaki masu muhimmanci kamar su ƙarafan kujeru da kuma katakon kujerun suna yin ɓatan dabo a makarantar.” A cewar sanarwar.

Sanarwar ta cigaba da cewa zargi ya faɗa kan shugaban makarantar wanda a baya sai da ƙungiyar iyayen yara da malamai ta PTA suka ɗora  alamar tambaya akan yadda yake gudanar da aikinsa.

A yanzu dai hukumar ta mayar da hankali wajen gano kayayyaki tare da tabbatar da cewa irin wannan almundahanar bata kawo na kasu ba a harkar inganta ilimi.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...