An hallaka a ƙalla mutum 60 a Zamfara ba gaira ba dalili

Rahotanni da suke fitowa daga arewa maso yammacin Najeriya a jiya na nuna cewa ƴan ta’adda sun kashe mutane sittin a ƙauyukan Jihar Zamfara.

Ƙauyukan da aka kai harin sun haɗa da Kurfa Danya, Kurfa Magaji Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki a ƙananan hukumomin Bukkuyum da Anka.

Jaridar ta ruwaito cewa mazauna ƙauyukan sun tabbatar mata da aukuwar lamarin inda mazaunansu suka arce don neman tsira.

Jihar ta Zamfara na fama da hare-haren ta’addanci, waɗanda suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da sace wasu da kuma raba su da muhallinsu.

More News

Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar. Hakan ya biyo bayan kudirin da dan...

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari a jihar. Jami’in hulda...

Sace-sacen motoci ya yawaita a Adamawa—Ƴan sanda

Ana ci gaba da samun karuwar sace-sacen motoci a jihar Adamawa, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar. Rundunar ‘yan sandan ta bayyana haka...

Majalisa ta gayyaci jagororin hukumomin tsaro saboda tashe-tashen hankulan da ake fama da su

A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu...