An gwabza ‘kazamin fada’ tsakanin sojoji da Boko Haram a Borno

sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gwabza kazamin fada da mayakan Boko Haram a ranar Laraba, lokacin da ‘yan ta-da-kayar-bayan suka yi yunkurin kutsa wa garin Gashigar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar Janar Texas Chukwu ya ce ‘yan ta-da-kayar-bayan sun je ne cikin manyan motoci guda tara, ‘ko da yake sun gamu da gamonsu a hannun dakarun kasar, inda suka yi musu fata-fata tare da haifar musu da asara ta mutane da kayan aiki.’

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce a yanzu haka dakarun sojin kasar sun mamaye yankin Gashigar da kewaye inda suke yin sunturi bayan faruwar lamarin.
Ta kuma bukaci da al’ummar yankin su kwantar da hankali tare da tabbatar musu da cewa suna cikin tsaro.A lokaci guda ita ma kungiyar IS a Afirka Ta Yamma ISWA, ta yi ikirarin kashe sojojin Najeriya bakwai tare da jikkata wasu a wani harin kwanton bauna ranar Larabar a garin Abadam.


Boko Haram a takaice

  • An kafa ta a shekarar 2002
  • Sunanta da Larabci shi ne, Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad
  • Ta fara aikinta ne da nuna kin jinin karatun boko
  • Ta kaddamar da kai hare-hare a shekarar 2009 da zummar samar da daular musulunci
  • Amurka ta ayyana ta a matsayin kungiyar ta’adda a 2013
  • Kungiyar ta ayyana wasu yankuna da ta kame a matsayin daulolin musulunci a shekarar 2014
  • A yanzu haka sojoji sun kwato mafi yawan yankunan
  • An samu rabuwar kai a shugabancin kungiyar tsakanin bangaren Shekau da na Al-Barnawi.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

ÆŠan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...