An aika Abdulrasheed Maina gidan kaso

bbc
Image caption

Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Okon Aban ya aike da tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdurrasheed Maina bayan da bukatar da lauyoyinsa suka gabatar ta neman beli ta gaza gamsar da kotun.

Lauyoyin gwamnati ne dai suka nemi kotun ta yi watsi da bukatar belin kasancewar Abdurrasheed Maina ya nemi belin ne tun ma kafin zaman kotun.

Yanzu haka an dage bukatar neman belin har sai zuwa ranar 30 ga watan Oktoban 2019, inda wanda ake karar zai sake bayyana.

Shi kuwa Faisal Abdulrasheed Maina wanda da ne ga Maina zai ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda har zuwa lokacin da zai sake gurfana a gaban kuliya ranar 6 ga watan Nuwamban 2019.

Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da Maina da dan nasa a gaban kuliya ranar Juma’a bisa tuhuma 12, inda shi kuma dan nasa ake tuhumar sa da laifuka uku.

A ranar Talatar da ta gabata ne kuma alkalin wata babbar kotu a Abuja, mai shari’a, Folashade Giwa Ogunbanjo ya bayar da umarnin cewa gwamnatin tarayya ta karbe kadarori guda 23 mallakar tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho a Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina.

Mai shari’a Ogunbanjo ya bayyana kwace kadarori mallakar Maina ne sakamakon wata kara da hukumar EFCC ta shigar, inda ta nemi da a mallaka wa gwamnati kadarorinsa na dan wani lokaci har zuwa lokacin da za ta kammala bincike.

Kadarorin mallakin Maina da kwacewar ta shafa sun hada da wadanda ke a Abuja da Kaduna da Sokoto da Borno.

Image caption

EFCC ta ce ta kama Faisal Abdulrasheed Maina ne tare da mahaifinsa a otal, inda ya tasar wa jami’anta da bindiga a hannunsa

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...