Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar, ya fitar da sanarwar umurtar Musulmi da su nemi jinjirin watan Shawwal 1444H daga yau Alhamis.
Sarkin ya yi fitar da wannan sanarwar ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini a Majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Junaidu a ranar Laraba.
A dokar addinin Musulunci dai, ganin jinjirin watan Shawwal shi ke alamta kawo ƙarshen watan Ramadan wanda Musulmi suke shafe dukkaninsa suna azumi a ciki.