An kashe dan jam’iyar NDC mutum guda tare da jikkata biyar a jihar Delta

Sulaiman SaadHausa1 minute ago

Mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu biyar suka samu raunuka bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari kan taron gangamin siyasa da magoya bayan jam’iyyar NDC suka shirya a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar a titin Nnebisi, lokacin da ƙungiyar Obidient/OK Movement ke gudanar da jerin gwano domin nuna goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da Bright Edafe, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Delta, ya fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce ta fara bincike domin gano yadda lamarin ya faru tare da tantance waɗanda ke da hannu a ciki.

‘Yan sandan sun ce tun kafin gangamin sun samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar tashin hankali, saboda haka suka gayyaci masu shirya taron zuwa wani zama na tsaro.

Sanarwar ta ce:

“Kafin a gudanar da gangamin, rundunar ta samu rahoton sirri da ke nuna yiwuwar tashin hankali, don haka aka gayyaci masu shirya taron zuwa wani taron tsaro.

“A yayin ganawar, an yi musu bayani kan barazanar tsaro da aka gano tare da shawartar su da su guji gudanar da jerin gwano a kan tituna.

“Haka kuma an ƙarfafa musu gwiwa da su gudanar da ayyukansu na siyasa a wani wurin da aka ware domin a samar musu da isasshen tsaro. Sai dai sun yi watsi da wannan shawara mai muhimmanci kuma suka ci gaba da yin jerin gwanon.”

Rundunar ta ce ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 12:15 na rana, inda ta tura jami’anta zuwa wurin da abin ya faru. Haka kuma an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.

‘Yan sandan sun kuma bayyana cewa har zuwa lokacin ba a tantance sunayen waɗanda abin ya shafa ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, Samuel Erale, ya yi Allah-wadai da tashin hankalin tare da kira ga jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji jerin gwano a kan tituna, sannan su riƙa tuntuɓar ‘yan sanda kafin gudanar da tarukan siyasa.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...