

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Dangyatin, ya ce zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027 wajibi ne ga mazauna jihar.
Dangyatin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam’iyyar APC a Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa goyon bayan Tinubu wani nauyi ne na addini, yana mai nuna cewa Shugaban ƙasar Musulmi ne, mataimakinsa ma Musulmi ne, kuma yana goyon bayan yankin Arewa.
Kakakin majalisar ya tuna rawar da Tinubu ya taka wajen tabbatar da nasarar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa ya dace Arewa ta rama wannan goyon baya.
Ya ce ” Tinubu ɗan’uwanmu Musulmi ne kuma jagora wanda ke da muradun al’ummar Jihar Jigawa a zuciya.”
Ya ƙara da cewa duk da cewa a farko ba a saka Jigawa cikin jadawalin kamfen ɗin Shugaban Ƙasa ba, yanzu Tinubu zai kai ziyara jihar.
“Saboda haka dole ne mu zaɓe shi kuma mu goyi bayan APC a kowane mataki,” a cewar Dangyatin.
Dangane da shirye-shiryen jam’iyyar, Kakakin ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ƙarfin APC, yana mai nuni da kasancewar tsoffin gwamnoni, sanatoci da mambobin majalisar tarayya a cikin jam’iyyar. Ya ce yawan mahalarta taron ya nuna irin faɗaɗɗen goyon bayan da APC ke da shi a faɗin Jigawa.
Dangyatin, wanda kuma shi ne mai jagorantar ƙungiyar City Boy Movement a Jigawa, ya ce ƙungiyar za ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin farko kafin zaɓen.
Ya ce mambobin ƙungiyar za su zagaya al’umma da gidaje domin bayyana wa jama’a ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Umar Namadi ke yi.
“Za mu yaɗa City Boy Movement a duk faɗin Jigawa, muna shiga gida-gida domin sanar da mutane abubuwan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnanmu suke yi.” a cewar Dangyati.