
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Abubakar Malami, ya yi Allah wadai da zargin cin zarafi da kai wa wasu mambobin tawagarsa hari a lokacin ƙaddamar da kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar a Birnin Kebbi.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar ranar Juma’a, Malami ya zargi wasu ’yan daba da kai wa ayarin tawagarsa hari, tare da lalata kayan aikin kafafen yaɗa labarai da kuma amfani da hayaki mai sa hawaye a wuraren da tawagar baƙi take.
Malami ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, musamman domin gano ko wasu hukumomin gwamnati ko jami’an tsaro na da hannu a ciki.
Ya kuma nemi gudanar da bincike na gaskiya kan rushe hedikwatar ƙungiyar Malami Pressure Group da ke kan titin Sani Abacha Bypass a Birnin Kebbi.
Ya ce duk da cewa gwamnatin jihar ta musanta hannu a rushe ginin, tana mai cewa rikicin mallakar kadarori ne ya jawo hakan, bai kamata wannan bayani ya hana gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar matakan da suka dace ba.
A cewarsa, saɓanin siyasa bai kamata ya zama dalilin tsoratar da mutane, lalata dukiyoyi ko hana jam’iyyun adawa gudanar da ayyukansu ba.
Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kebbi, hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a siyasa da su mutunta ’yancin faɗar albarkacin baki, haɗuwa da jama’a da gudanar da tarurrukan lumana, domin bai wa ’yan ƙasa damar shiga harkokin siyasa cikin ’yanci.
Malami ya kuma jero matsalar ’yan bindiga, ƙauracewar al’umma daga muhallansu, talauci, ƙarancin abinci da kuma tangardar ayyukan noma a matsayin manyan ƙalubalen da ke addabar Jihar Kebbi.
Ya bukaci gwamnati ta mayar da hankali wajen kare manoma, inganta ilimi da kiwon lafiya, rage tsadar rayuwa da samar da damarmaki ga matasa.
A ƙarshe, ya shawarci magoya bayan ADC da su kasance masu zaman lafiya da bin doka, yana mai cewa duk wani harkar siyasa ya kamata a gudanar da shi bisa ƙa’ida.