
Wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Divine Dung Davou, mai shekaru 18, wanda ke aikin tsaron sa-kai a ƙauyen Rachas da ke gundumar Heipang, Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren Talata, inda harin ya jefa mazauna yankin cikin alhini da fargaba kan matsalar tsaro da ke addabar yankunan karkara.
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, ne ya tabbatar da kisan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya ce bayanan da ƙungiyar ta samu sun nuna cewa wasu mahara ɗauke da makamai ne suka kai harin, inda suka kashe Divine, wanda ke aikin sa-kai domin kare al’ummarsa.
Wani shugaban al’umma a Rachas, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mutuwar matashin ta girgiza jama’a, yana mai cewa ya shiga aikin tsaron sa-kai ne saboda babu jami’an tsaro da ke sintiri a ƙauyen da daddare.
Ya ce: “Mun shiga cikin baƙin ciki matuƙa. Divine ɗan shekara 18 ne kawai. Ya shiga aikin sa-kai domin kare ƙauyenmu saboda ba mu da jami’an tsaro a nan da daddare. Yanzu an kashe shi yana ƙoƙarin kare mu. Kada gwamnati ta yi watsi da mu.”
Wata mazauniyar yankin, Mary Chollom, ta ce harin ya dawo da fargaba a zukatan jama’a, inda ta bayyana cewa karar harbe-harbe ta hana su barci a daren da abin ya faru.
Ta ce mafi yawan mazauna yankin manoma ne, kuma suna rayuwa cikin tsoron hare-hare, don haka ta yi kira ga gwamnati da ta tura jami’an tsaro yankin.
Shi ma wani matashi a yankin, Dalyop Gyang, ya yi kira da a kamo waɗanda suka aikata kisan tare da tabbatar da an yi musu hukunci.
A martanin da ta mayar, ƙungiyar Berom Youth Moulders Association ta buƙaci rundunar ’yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa, su kamo waɗanda suka kashe matashin, sannan su ƙarfafa sintiri da tattara bayanan sirri a yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su ɗauki matakai na dindindin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a wuraren da ake yawan kai hare-hare.
Ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin da al’ummar Rachas, tare da kira da a ɗauki matakan da za su hana sake aukuwar irin wannan lamari.
Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato kan lamarin bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.