Ana Fargabar ’Yan Sanda Biyar Sun Mutu Bayan ’Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocinsu Hari


Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda biyar da ke tafiya daga Jihar Sakkwato zuwa Jihar Zamfara domin gudanar da wani aiki na musamman.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne ranar Lahadi, lokacin da jami’an, waɗanda ke cikin motoci uku, suka faɗa tarkon ’yan bindigar da suka yi musu kwanton ɓauna.

Wani jami’in ɗan sanda da ke cikin tawagar, amma ya tsira daga harin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun buɗe wa motar da ke ƙarshen ayarin wuta ba zato ba tsammani.

Jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa abokan aikinsa biyar ne suka rasa rayukansu a harin.

Ya ce: “Muna tafiya ne cikin motoci uku, sai kwatsam suka buɗe wa motar da ke ta uku a bayanmu wuta. An kashe jami’anmu biyar a wannan harin.”

Ya ƙara da cewa an tura mafi yawan jami’an ne domin gudanar da wani aiki na musamman a Jihar Zamfara lokacin da aka kai musu harin.

Wasu bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna gawarwakin wasu daga cikin jami’an a cikin mota, inda aka ga an ɗaure hannayensu da ƙafafunsu da igiya.

Bidiyoyin sun kuma nuna kayayyakin jami’an a warwatse a wurin da lamarin ya faru, yayin da aka ga alamun jini a motar da suke ciki.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin shiyya ta 10 ta rundunar ’yan sanda, ASP Abdallah Faruku, bai yi nasara ba, domin ba a samu damar shiga wayarsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, rundunar ’yan sanda ba ta fitar da cikakken bayani a hukumance kan harin ba.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...