Gwamnatin Sokoto ta rufe ginin ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyar ADC

Sulaiman SaadHausa, Arewa19 minutes ago



Gwamnatin Jihar Sakkwato ta rufe ɗaya daga cikin ofisoshin jam’iyyar ADC a jihar.

Kwamishinan ƙasa da gidaje na jihar, Barrista Nasiru Dantsoho, wanda ya sanar da rufe ginin a ranar Litinin, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kare rayuka da dukiyoyi bayan wata tarzoma da ta auku kwanan nan tsakanin magoya bayan jam’iyyar da wasu bata-gari.

Dantsoho ya yi  zargin cewa bayan gwamnatin jihar ta sake duba takardun da suka shafi ginin ofishin, ta gano cewa asalin ginin mallakin tsohon Bankin Savannah ne, kuma babu wata hujja a hukumance da ke nuna an canja masa takardun mallaka.

Ya ce gwamnati ta rubuta wasiƙa zuwa ga Hukumar Kula da Inshorar Ajiyar Kuɗaɗe ta Najeriya (NDIC) wacce  ta bayyana a matsayin mai riƙon kadarar, tana neman bayani kan wanda ke mallakar ginin a halin yanzu, amma har yanzu ba a samu amsa ba.


“Bayan sake duba takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy) da sauran muhimman takardu, mun gano cewa wannan gini mallakin Bankin Savannah ne, kuma har zuwa yau babu wani canjin mallaka da aka yi a hukumance.

“Mun rubuta wasiƙa ga NDIC, wadda ke kula da wannan gini, domin ta fayyace wanda yake da mallakarsa a yanzu, amma har yanzu ba mu samu amsa ba.”

Kwamishinan ya ce gwamnati ta yanke shawarar rufe ginin har sai NDIC ta bayar da amsar da ake jira, yana mai cewa hakan ya zama dole domin hana sake aukuwar tashin hankali tare da kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma yi kira ga duk wanda ke da’awar mallakar ginin da ya gabatar da takardun da suka dace ga gwamnati domin tantancewa da yin rajistar da ta dace. Bayan haka ne za a miƙa ginin ga wanda ya tabbatar da haƙƙin mallakarsa.

Sai dai Dantsoho ya jaddada cewa kadarar za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar har sai an warware matsalar wake da ikon  mallakar ginin

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya yi yunƙurin shiga cikin ginin da aka rufe da ƙarfin tsiya zai fuskanci matakan doka da suka haɗa da gurfanar da shi a gaban kotu.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙara tsamin siyasa a Jihar Sakkwato, sakamakon zarge-zargen hare-hare da suka shafi magoya bayan jam’iyyar ADC da jami’an rundunar tsaro mallakin gwamnati.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...