
Gwamnatin Tarayya ta umarci cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin Najeriya da su ƙarfafa dakunan killace masu fama da cututtuka tare da tanadar da kayan kariya da sauran muhimman kayayyakin jinya, domin shirin tunkarar duk wata yiwuwar ɓullar cutar Ebola.
Mataimakin Shugaban Sashen Ayyukan Lafiya na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), da ke Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Yunus Mohammed Eze, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai.
Ya ce Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ce ta aika da umarnin ga asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin ƙasar, inda ta buƙace su da su tanadi matakan gaggawa domin gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar, killace su da kuma kula da lafiyarsu.
A cewarsa, asibitin FMC Birnin Kudu ya bi umarnin ta hanyar ƙarfafa sashen killace masu cututtuka tare da sanya ma’aikatan lafiya cikin shirin ko-ta-kwana.
Dakta Eze ya ce: “Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Lafiya, ta sanar da cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin ƙasar tare da umartar su da su shirya dakunan killace masu cututtuka, kuma su tabbatar da samun dukkan kayan da ake buƙata domin kare ma’aikatan lafiya da kula da marasa lafiya.
“Mun karɓi umarnin, kuma nan take shugabancin asibitin ya fara aiwatar da shi. Mun ƙarfafa sashen killace masu cututtuka, kuma a shirye muke mu killace duk wanda ake zargin ya kamu da cutar tare da tura shi wata cibiyar kula da masu cutar idan buƙatar hakan ta taso.”
Ya ƙara da cewa asibitin ya kuma tsara yadda za a tura waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ko waɗanda aka tabbatar sun kamu zuwa cibiyoyin da aka ware domin kula da masu cutar.
Dangane da wayar da kan jama’a, Dakta Eze ya ce asibitin ya ƙara ƙaimi wajen ilmantar da al’umma ta hannun sashen yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa da kuma sashen kula da lafiyar al’umma.
Ya bayyana cewa asibitin na haɗin gwiwa da Kamfanin Yaɗa Labarai na Jihar Jigawa domin wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya daga cututtuka da kuma muhimmancin kai rahoton duk wata alama da ake zargin tana da alaƙa da cutar cikin gaggawa.
Ya kuma ce ma’aikatan lafiya na ci gaba da wayar da kan marasa lafiya da baƙi a asibitin, tare da ƙarfafa musu gwiwar isar da bayanan ga iyalansu da sauran al’umma.