Fadar Shugaban Ƙasa Ta Zargi Wani Mutum Da Samar Da Wata Ma’aikatar Gwamnati Ta Bogi

Fadar shugaban ƙasa ta zargi Adeyemi Adeniyi Mathew da kasancewa ɗan damfara da ya naɗa kansa shugaban wata hukumar neman tallafi daga ƙasashen waje tare da buɗe ofis a ginin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya.

Adeyemi ya yi ikirarin cewa mai bai wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa shawara ne ya naɗa shi a mukamin, amma shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya musanta wannan zargi.

Gwamnatin tarayya ta kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su guji yaɗa jita-jita ko yin shaci-faɗi kan lamarin, tana mai cewa batun yana gaban kotu domin ci gaba da shari’a.

More from this stream

Recomended