Gwamnatin tarayya ta ce kamfanonin da ke samar da siminti ba sa yin abin da ya dace wajen dakile hauhawar farashin siminti a kasar.
Gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta amince da yanayin da farashin kayan gini kamar siminti ke ci gaba da tashi ba tare da kayyadewa ba.
Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Dangiwa, ya bayyana haka a lokacin da ya gayyaci masu sana’ar siminti zuwa wani taro a hedkwatar ma’aikatar da ke Abuja, a ranar Talata 20 ga Fabrairu, 2024.
Arc. Dangiwa ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda farashin siminti da sauran kayayyakin gini ke ci gaba da tabarbarewa, sannan ya zargi kamfanonin da ke fakewa da canjin kudi da cewa su ke wahalar da ‘yan Najeriya.