Ƴan Sanda Sun Kama Fasto da Abokin Hulɗarsa Kan Zargin Satar Mota a Abuja



Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani fasto mai suna Edwin Nwabueze da wani mutum mai suna Sadiq Jamiu bisa zargin hannu a satar motar Toyota Camry a Abuja.

An ruwaito cewa an sace motar ne a harabar UTC Plaza da ke yankin Garki a babban birnin tarayya.

A cewar rundunar ’yan sandan, an kama Nwabueze a gidansa ranar 27 ga Oktoba, 2026, bayan gudanar da bincike kan satar motar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan FCT, Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Nwabueze ya bayyana kansa a matsayin fasto a cocin Salvation Power Bible Ministry da ke yankin North Bank a Jihar Benuwai. An kuma bayyana cewa shi ɗan asalin ƙaramar hukumar Oji River ne a Jihar Enugu, amma yana zaune a Benuwai.

Rundunar ta ce bayan kama shi, Nwabueze ya jagoranci jami’an tsaro zuwa wani wuri, inda suka kama wanda ake zargin abokin harkarsa ne, Sadiq Jamiu.

Binciken farko ya kuma danganta Nwabueze da wasu kamun da rundunar ’yan sandan Jihar Benuwai ta taɓa yi masa a baya kan zargin satar motoci.

Sanarwar ta ƙara da cewa bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin mambobi ne na wata ƙungiyar masu satar motoci da ke aiki tsakanin jihohi, inda suke satar motoci tare da sayar da su a wurare daban-daban.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano cikakken ayyukan ƙungiyar da kuma cafke sauran waɗanda ake zargin suna cikinta, waɗanda har yanzu suke tsere.

Ta tabbatar da cewa waɗanda aka kama suna tsare a hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...