Kwamitin gwamnatin tarayya ya bada shawarar biyan naira biliyan ₦1.4 ga iyalan masu haƙar ma’adanai da suka mutu a Niger



Kwamitin gwamnatin tarayya da ke binciken mutuwar mutum 37 da ake zargin masu haƙar ma’adanai ne  ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka mutu yayin da suke tsare a hannun jami’an Hukumar Tsaro Ta Civil Defense ta Najeriya (NSCDC)a Minna, jihar Neja, ya ba da shawarar a kori manyan jami’an da ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Jonathan Kure, shugaban kwamitin mai mutum 10, ya bayyana hakan a ranar Talata yayin gabatar da rahoton kwamitin ga Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida, a Abuja.

Kure ya ce kwamitin ya ba da shawarar a biya iyalan mutane 33 da suka mutu da kuma mutum 44 da suka tsira diyya ta naira biliyan 1.4.

Ya ce mutuwar waɗannan mutane abin da za a iya kauce wa ne, yana mai cewa an tsare su cikin yanayi marar daraja, ciki har da yara ƙanana 14.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar a sallami kwamandan NSCDC na jihar Neja tare da sauran jami’an da suka taka rawa kai tsaye wajen tsare masu haƙar ma’adanan har ta kai ga  mutuwarsu. Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar domin ƙarfafa shugabancinta.

Tunji-Ojo, wanda ya karɓi rahoton, ya yi alƙawarin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton domin tabbatar da an yi wa duk waɗanda lamarin ya shafa adalci.

Har ila yau, ya umarci kwamandan NSCDC da ya dakatar da duk jami’an da suka share ko suka gyara wurin da aks tsare mutanen, bisa zargin cewa sun yi hakan ne domin lalata shaidu.

A baya dai jaridar TheCable ta ruwaito cewa kwamitin binciken ya gano cewa masu haƙar ma’adanan sun mutu ne sakamakon rashin isasshen iskar oxygen , har ta kai ga   jikin mutanen ya rasa iskar da yake buƙata domin rayuwa.

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin ne a ranar 19 ga Satumba bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da bayyana gaskiya kan mutuwar mutanen.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...