
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta kama wani direban motar makaranta mai shekaru 28, Onome Ughagha, bisa zargin sace wata ɗaliba ’yar shekara 14 da yi mata fyade a garin Sapele na jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya nemi kuɗin fansa naira 503,000 daga mahaifin ɗalibar, kuma ya karɓi kuɗin kafin sakin yarinyar.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Ya ce mahaifin yarinyar ne ya kai rahoton lamarin ga ofishin ’yan sanda na yankin Sapele ranar Talata.
A cewar sanarwar, mahaifin ya yi zargin cewa an sace ’yarsa ne yayin da take shirin tafiya makaranta. Daga bisani, wanda ake zargin ya kira shi, ya nemi naira 503,000 tare da yi masa barazanar kashe yarinyar idan bai biya kuɗin ba.
Bayan karɓar kuɗin, an ce an bar yarinyar a kan titin Oton da ke Sapele, inda ta sake haɗuwa da iyalanta cikin halin firgici, tare da alamun cewa an yi mata lalata. An kai ta wani asibiti domin duba lafiyarta da ba ta kulawar da ta dace.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun fara bincike tare da gayyatar shugaban makarantar da mataimakinsa domin yi musu tambayoyi. A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya bar motar makarantar ya tsere, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen nemansa.
Daga bisani, bisa sahihan bayanan sirri, jami’an ’yan sanda sun gano shi a maboyarsa da ke yankin Ajimele na Sapele, inda suka kama shi ranar Juma’a. Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya amsa hannu a laifin yayin tambayoyin farko.
Rundunar ta ce ana shirin miƙa shi ga sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Asaba domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Samuel Erale, ya yi Allah-wadai da lamarin, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike kuma za a hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.
Ya kuma yi kira ga shugabannin makarantu, iyaye da masu harkar sufuri da su ƙara sa ido wajen kare yara, yana mai jaddada cewa tsaron duk yaron da aka damƙa musu amana ya kamata ya zama babban abin da suke ba muhimmanci.