

‘Yan bindiga dake ɗauke da makamai a kama babura sun kai farmaki wani ƙauye dake jihar Taraba dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe aƙalla mutum 20, kamar yadda waɗanda suka tsira daga harin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Asabar.
Mazaunan yankin sun ce maharan sun fara harbin kan me uwa da wabi jim kaɗan bayan sallar Juma’a a ƙauyen Binnari da ke jihar Taraba.
Arewa maso gabashin Najeriya ya daɗe yana fama da matsalar tayar da ƙayar baya ta masu iƙirarin jihadi. Sai dai jihar Taraba, wadda ke kusa da tsakiyar ƙasar, tana kuma fuskantar hare-haren ‘yan bindiga marasa wata manufa ta addini.
‘Yan bindiga kan kai hare-hare a ƙauyuka, su yi garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, sannan su tilasta wa manoma ko masu haƙar ma’adanai biyan haraji a yankunan karkara inda gwamnati ba ta da cikakken iko.
“Duk mutane su riƙa gudu ta ko’ina don tsira daga harin. Babu wanda ya san inda zai samu mafaka mai aminci,” in ji wani mazaunin Binnari mai suna Isiyaku Musa.
Shi da Sa’idu Nuhu sun ce adadin waɗanda suka mutu ya haura 20.
“Bayan maharan sun tafi, mun ƙirga gawarwaki sama da 20, sannan har yanzu akwai wasu da ba a san inda suke ba,” in ji Nuhu ga AFP.
Sai dai rundunar ‘yan sanda ta bayar da ƙaramar ƙididdiga, inda ta ce an gano gawarwakin mutum 10 zuwa yammacin ranar Juma’a.
Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International Nigeria ta ce: “Hukumomin Najeriya na ci gaba da barin al’ummomin karkara a wasu sassan arewacin ƙasar cikin mawuyacin hali, inda ‘yan bindiga ke aikata munanan laifuka ba tare da hukunci ba.”
Ta ƙara da cewa, “Gazawar hukumomi na gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata irin waɗannan laifuka gaban shari’a tana ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da aikata laifuka ba tare da tsoro ba.”
Wani jagoran al’umma, Malam Abubakar Saifullahi, ya ce maharan sun zo ne a kan babura kusan 50, mutum biyu a kan kowane babur, kafin su kutsa cikin ƙauyen.
“Sun kwashe kaya daga shaguna tare da satar kuɗi, kayan abinci da sauran kayan masarufi. Haka kuma sun tafi da baburan da mutane suka bari yayin da suke gudun ceton rayukansu,” in ji Saifullahi.
Matsalar ‘yan bindiga tana ƙara tsananta a yankunan Arewa maso Yamma da Tsakiyar Najeriya, inda manyan ƙungiyoyin masu laifi da kuɗi ke motsawa suke fafatawa da jami’an tsaro a yankunan karkara masu wahalar isa.
A wani labarin dabam kuma, rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Asabar cewa ta kashe mutane 15 da ta bayyana a matsayin “‘yan ta’adda” a wani harin sama da aka kai a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas.
Najeriya dai tana yaƙi da masu tayar da ƙayar baya tun bayan bore na ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2009.