Obasanjo Ya Zargi Sauye-Sauyen Tinubu Da Kara Jefa ’Yan Najeriya Cikin Talauci

Muhammadu SabiuHausa24 minutes ago



Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya soki sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar, yana mai cewa faduwar darajar Naira ta rage karfin sayen kayayyaki ga ’yan Najeriya tare da kara tsananta talauci.

Obasanjo ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron koli na Financial Times Africa Summit 2026 da aka gudanar a birnin Landan na Birtaniya, inda ya soki matakin gwamnatin Tinubu na rage darajar Naira a shekarar 2023.

Tsohon shugaban kasar ya ce faduwar darajar kudin ta jefa ’yan Najeriya cikin talauci, yana mai nuni da yadda darajar Dala ta tashi daga kusan Naira 500 zuwa Naira 1,500.

“Ba mu rayuwa a matsayin kasa da ta ware kanta daga sauran duniya. Muna mu’amala da sauran kasashe. Amma cikin dare daya, ka rage darajar kudinka da kashi 300 cikin 100. Naira ta tashi daga Naira 500 kan Dala daya zuwa Naira 1,500. Abin da hakan ke nufi shi ne, an talauta kowane dan Najeriya da kashi 300 cikin 100,” in ji Obasanjo.

Ya ce halin da ake ciki ya sa ake kallon Najeriya a matsayin kasar da ke da yawan mutanen da ke rayuwa cikin talauci, inda ya kalubalanci masu ganin cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin na da amfani ga kasar.

“Ba za ka ce mini hakan alheri ne ga Najeriya ba. Ba za ka ce mini hakan alheri ne gare mu ta kowace fuska ba,” in ji shi.

Obasanjo ya kuma nuna shakku kan kiraye-kirayen da ake yi na bai wa gwamnatin Tinubu karin lokaci domin aiwatar da manufofinta, yana mai cewa bai ga wani gagarumin sauyi na alheri a tattalin arzikin kasar ba.

“Game da tattalin arziki, ban ga wani abu da ke kara inganta ba. Wadanne manufofi kuke ganin ana aiwatarwa? Ka talauta jama’arka, sannan kana son ci gaba da aiwatar da abin da ke kara jefa su cikin talauci?” ya tambaya.

Ya kara da cewa manufofin gwamnatin ba su kasance cikin maslahar ’yan Najeriya ba.

Dangane da cire tallafin man fetur, Obasanjo ya amince cewa man fetur na da muhimmanci ga harkokin tattalin arziki, amma ya ce ya kamata gwamnati ta fara magance cin hanci da rashawa da ke tattare da tsarin tallafin kafin cire shi.

Ya ce kasa da ke fuskantar matsanancin kalubalen tattalin arziki ya kamata ta dakile cin hanci da rashawa, almubazzaranci da kashe-kashen da ba su da muhimmanci, sannan ta mayar da hankali kan samar da kayayyaki.

Bayanan da rahoton ya ambata sun nuna cewa kafin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya hade hanyoyin musayar kudaden waje a ranar 14 ga Yuni, 2023, farashin Dala a hukumance ya kai kusan Naira 460.80. Zuwa ranar 19 ga Oktoba, farashin ya kai kusan Naira 1,333.54, yayin da ya taba kaiwa Naira 1,607.05 a farkon watan Mayun 2025.

A wani bangare kuma, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 14.63 cikin 100 a watan Satumban 2026, daga kashi 20.98 cikin 100 a daidai wannan lokaci na shekarar da ta gabata. Sai dai hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 19.59 cikin 100, yayin da tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kashi 4.43 cikin 100 a rubu’in biyu na shekarar.

Ministan Kudi kuma mai kula da tattalin arzikin kasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana a ranar 19 ga Agusta cewa cire tallafin man fetur ya taimaka wa gwamnati wajen tara Naira tiriliyan 15.8 tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025.

Rahoton ya ce an yi kokarin samun martanin Fadar Shugaban Kasa kan sukar Obasanjo, amma ba a samu nasara ba, saboda ba a iya tuntubar Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan yada labarai da dabarun sadarwa.

Loading

Signing-in 3 seconds...

Signing-up 3 seconds...