An Harbe Sanannen Malamin Addini A Pakistan



Ƴan sanda a ƙasar Pakistan sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kashe wani fitaccen malamin addinin Musulunci a lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Rahotanni sun ce Maulana Muhammad Idrees na kan hanyarsa ta komawa gida ne daga wata makarantar koyar da addini, lokacin da ƴan bindigar da ke kan babura biyu suka buɗe masa wuta, inda suka kashe shi nan take.

Harin ya faru ne a yankin Charsadda, inda kuma aka jikkata ƴan sanda biyu da ke cikin tawagar da ke ba shi tsaro.

Ya zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin. Sai dai galibi ana danganta irin waɗannan hare-hare da masu tsatsauran ra’ayin addinin Musulunci.

More from this stream

Recomended