Gwamnatin jihar Edo ta ce mutane 56 ne suka kamu da cutar zazzaɓin Lassa a jihar a yayin da mutane 8 suka mutu a tsakanin ranar 30 ga watan Disamba 2024 da kuma Janairun 2025.
Da yake magana a wurin wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Benin babban birnin jihar, Cyril Oshiomhole kwamishinan lafiya na jihar ya ce ɓarkewar cutar na yin babbar barazana ga tsarin kiwon lafiyar al’umma matukar ba a dakile ta ba.
“Annobar cutar ta 2025 ta fara ne a ranar 30 ga watan Disamba tun daga sannan an yi gwajin mutane 336 inda aka tabbatar da 56 na da cutar kuma mutane 8 suka mutu,”
Oshiomhole ya ce a yanzu haka marasa lafiya 14 na can na samu kulawa ta musamman daga likitoci a Cibiyar Lura da Zazzaɓin Lassa dake asibitin koyarwa na Irrua.