Mafarauta sun gano gawarwakin ƴan fashin daji biyu a Kaduna

Rahotannin sun bayyana cewa wasu mafarauta sun gano wasu gawarwaki biyu da ake zargin na ƴan fashin daji ne da suke tserewa farmakin da sojoji suke musu a dajin Kurmin-Kare  dake ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan fashin daji  uku aka kashe  yayin wata musayar wuta tsakaninsu da sojoji a ƙauyen Mai Iddo a ranar Asabar da ta gabata a yayin farmaki kan wata maɓoyar su inda aka ceto wasu manoma huɗu da aka yi garkuwa da su ciki har da wata mace guda ɗaya.

Wani jagoran al’umma a garin a zantawar  da aka yi da shi ta wayar tarho ya  tabbatar da gano gawarwakin biyu da mafarautan suka yi.

Ya ce wasu mafarauta biyu daga ƙauyen Kurmin-Kare mai maƙotaka damu su ne suka gano gawarwakin biyu akan wani dutse.

“Dagacin ƙauyen ne ya zo wurina da rana ya ke cemin mafarauta sun gano gawarwaki biyu da ake zargin na daga cikin ƴan bindigar da suka tsere daga ƙauyen Mai Iddo bayan musayar wuta a sojoji,” ya ce.

Kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa ba kan batun.

A cewarsa gawarwakin biyu sun yi kaca-kaca da harbin bindiga.

More from this stream

Recomended